Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 17:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ko haifaffe a gidanka ko an sayo da kuɗi, dole a yi musu kaciya. Alkawarina cikin jikinku zai kasance madawwamin alkawari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 17:13
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.


Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.


A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir'auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir'auna.


Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.


Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, 'ya'yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa 'ya'yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin 'ya'yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”


“Wanda ya saci mutum, ya sayar, ko kuwa a iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.


Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa 'ya'ya mata ko maza, to, matar da 'ya'yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.


Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a 'yantar da shi kyauta.


Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir'auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma'ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.


Ku zo mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan'uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” 'Yan'uwansa suka yarda da shi.


Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”


Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan.


Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”


“Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.


Amma idan firist ya sayi bawa da kuɗinsa, bawan ya zama dukiyarsa, bawan zai iya ci, haifaffun gidansa kuma za su iya cin tsattsarkan abincin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ