Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,
Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.
Sa'an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.”
Idan baƙon da yake zaune tare da ku yana so ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji tare da ku, to, sai a yi wa kowane namiji da yake a gidansa kaciya sa'an nan ya iya shiga idin, shi kuma ya zama ɗan ƙasa. Daɗai, marar kaciya ba zai ci ba.