Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 16:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?” Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 16:8
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”


Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.


Idan mai mulki ya husata da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.


Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’


Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine.


Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu.


Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”


A can ya shiga wani kogo domin ya kwana. Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”


Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”


Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.


Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”


Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ