Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 16:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 16:2
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa 'ya'ya mata ko maza, to, matar da 'ya'yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.


Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.


Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.


'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.


Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,


Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.


Ishaku kuwa ya yi addu'a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki.


Gama dā Allah ya kulle mahaifar dukan gidan Abimelek saboda Saratu matar Ibrahim.


Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.”


Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.”


Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.


Sai 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko'ina a duniya.


Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato ba ta da ɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ