Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran.
A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan'ana sa'ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa.
Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.
A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.