Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
Mutanen da suka keta alkawarina, ba su kuma kiyaye maganar alkawarin da suka yi a gabana ba, sa'ad da suka raba ɗan maraƙi kashi biyu, suka bi ta tsakiyarsa,