Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.
To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai ake yi wa, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Gama abin da muke cewa shi ne, “Aka lasafta bangaskiyar Ibrahim adalci ce a gare shi.”
Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,
wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.
Ka iske shi amintacce a gare ka, Ka kuwa yi masa alkawari. Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana, Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa, Ta zama inda zuriyarsa za su zauna. Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.