Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 15:16 - Littafi Mai Tsarki

16 A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 15:16
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya yi abar banƙyama ƙwarai, ya bi gumaka kamar yadda Amoriyawa suke yi, waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban Isra'ilawa.


“A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.


suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.


Zaman da Isra'ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin.


Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani lalle ne zuriyarka za ta yi baƙunci cikin ƙasar da ba tata ba ce, za ta kuwa yi bauta, za a kuma tsananta mata har shekara arbaminya,


Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu.


“Tun da yake Manassa, Sarkin Yahuza, ya aikata waɗannan abubuwa masu banƙyama, ya kuma aikata mugayen abubuwa fiye da dukan abin da Amoriyawa, waɗanda suka riga shi, suka aikata, ya kuma sa mutanen Yahuza su yi zunubi saboda gumakansa,


shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,


Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka.


Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”


Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.


A wannan rana kuka fita, wato a watan Abib.


“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.


Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.


Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa, Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ