Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.
Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.
Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.