A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama'ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’
ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’
Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.
Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala'ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can.
Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”
Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.
Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada’ ”
Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.