tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha'awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki. Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.
Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.
Haka kuma maza suka bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”
Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.
ya kuma umarce ka ka tafi ka hallakar da waɗannan mugayen mutane, wato Amalekawa. Ya faɗa maka ka yi yaƙi, har ka hallaka su ƙaƙaf, kada ka rage ko guda ɗaya.
Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”
Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”