Farawa 12:15 - Littafi Mai Tsarki15 Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da suke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da suke gaɓar Bahar Rum da waɗanda suke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da suke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.