Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 12:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 12:11
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce.


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.


Sa'ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai.


Ƙaunataccena kamar furen jeji yake Wanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.


Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.


ya ce, matarsa Saratu 'yar'uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu.


Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.


sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.


A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”


Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.


Ko da yake yarinyar kyakkyawa ce ƙwarai, ta zama mai lura da sarki, ta kuwa yi masa hidima, amma sarki bai yi jima'i da ita ba.


Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ