Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”
Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba?
“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina kawo muku Wata al'umma daga nesa,” in ji Ubangiji, “Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun zamanin dā. Al'umma wadda ba ku san harshenta ba, Ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.
Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,
Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.”