Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kalidiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can.
Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.
Kakannina sun hallakar da biranen Gozan, da Haran, da Rezef, suka kuma kashe mutanen Eden, mazaunan Telassar, ba ko ɗaya daga cikin gumakansu da ya iya cetonsu.