Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 11:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 11:2
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke.


Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.


A zamanin Amrafel Sarkin Shinar, shi da Ariyok Sarkin Ellasar, da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim,


Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa'ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.”


A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.


Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna.


Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.


A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ