16 Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,
16 Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.
Nahor ɗan Serug, Serug ɗan Reyu, Reyu ɗan Feleg, Feleg ɗan Eber, Eber ɗan Shela,
'Ya'ya biyu maza ne aka haifa wa Eber. Sunan ɗayan Feleg, saboda a lokacinsa ne aka karkasa duniya, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan.
Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim, Za su wahalar da Assuriya da Eber, Su kuma da kansu za su lalace.”
An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan.
An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, 'ya'ya, shi ne kakan 'ya'yan Eber duka.
Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.