A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”
Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su.