Ku haura, ku dawakai, Ku yi sukuwar hauka, ku karusai! Bari sojoji su fito, Mutanen Habasha da Fut masu riƙon garkuwoyi, Da mutanen Lud, waɗanda suka iya riƙon baka.
A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.