gama jiragen ruwa na Kittim za su tasar masa, shi kuwa zai ji tsoro, ya janye. “Zai koma ya huce fushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai kula da waɗanda suka yi banza da tsattsarkan alkawarin.
Wannan shi ne jawabi a kan Taya. Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.
Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan. Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim, Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.
An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar, Don ya zama alama. An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.