Ku ta da tuta a duniya, Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho, Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita, Ku kirawo mulkokin Ararat, da na Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita. Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai shugabanci yaƙin da za a yi da ita, Ku kawo dawakai kamar fāra.