Zan kawar da jininsu daga bakinsu, Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu. Sauransu za su zama jama'ar Allahnmu, Za su zama kamar sarki cikin Yahuza. Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.
Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.
“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.