Za su mallaki ƙasar Assuriya da takobi, Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da zararren takobi, Zai cece mu daga hannun Ba'assuriye, Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu yaƙi, Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.
Assuriya ba za ta cece mu ba, Ba kuwa za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, ‘Kai ne Allahnmu,’ ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”
sai suka tafi wurin Zarubabel, da shugabannin gidajen kakanni, suka ce musu, “Ku yarda mana mu yi ginin tare, gama muna yi wa Allahnku sujada kamar yadda kuke yi, muna kuma ta miƙa masa sadaka tun kwanakin Esar-haddon, Sarkin Assuriya, wanda ya kawo mu nan.”