4 Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,
4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu.
Haske yana da daɗi, abu mai kyau kuma idanu su dubi hasken rana.
To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.
su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau.
Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.
Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Shi mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin dukan abin da ya halitta.
Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka, Jama'arka kuma za su yi maka godiya!
Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.