Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 1:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 1:24
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ga dorina wanda ni na halicce ta, Kamar yadda na halicce ka, Tana cin ciyawa kamar sa.


Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu.


da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.


Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji, Masu rarrafe da tsuntsaye!


“Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so? Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,


su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.


Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu, Su yi ta aiki har maraice ya yi.


A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama, Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.


“Kai ka yi wa doki ƙarfinsa? Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza?


“Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki? Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?


“Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa? Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?


Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.


Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ