17 Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,
17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya,
Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi, Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
Ya Ubangiji, Ubangijinmu, An san girmanka ko'ina a dukan duniya. Yabonka ya kai har sammai,
“Ayuba, a dukan kwanakinka Ka taɓa umartar wayewar gari, Ko ka sa alfijir ya keto?
Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce, “ ‘Na sa ka haske ga al'ummai, Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”
na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya.
idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,
Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da take mulkin sammai da duniya ba,