Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 1:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 1:12
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙasa da kanta takan ba da amfani, tsiro shi ne na farko, sa'an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan.


Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.


Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.


Shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, ya riɓanya shi, ya kuma yawaita albarkar ayyukanku na alheri.


Ba shakka, Ubangiji zai ceci jama'arsa, Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma. Dukan al'ummai kuwa za su yi yabonsa.


Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.


Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.


Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.


Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu, Tsire-tsire kuma don amfanin mutum, Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ