Ubangiji ne ya halicci sammai, Shi ne wanda yake Allah! Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta, Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo! Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba, Amma wurin zaman mutane. Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah, sai ni.
“Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko, Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa, Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”
Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.
Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce, “Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji, Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama. Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu, Ka ba dukansu rai, Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.
“Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku. Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu. Ni kaɗai na shimfiɗa sammai, Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.
Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”
“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.
duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.
Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.
ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,
Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,
ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.
A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.
Ka dubi sararin sama a bisa! Wane ne ya halicci taurarin da kake gani? Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji, Ya sani ko su guda nawa ne, Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!
Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.
Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku, Wanda ya shimfiɗa sammai, Ya kuma kafa harsashin ginin duniya? Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku, Da waɗanda suke shiri su hallaka ku? Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.
Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.