Ezra 9:13 - Littafi Mai Tsarki13 Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 “Abubuwan nan sun faru da mu sakamakon mugayen ayyukanmu ne, amma duk da haka ya Allahnmu, ba ka ba mu horo bisa ga yawan zunubanmu ba, ka kuma bar mana saura. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.