To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.
Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”
Gama mu bayi ne, duk da haka Allahnmu bai manta da mu a bautarmu ba, amma ya sa muka sami tagomashi a wurin sarakunan Farisa, suka iza mu domin mu gina Haikalin Allahnmu, mu sāke gyaransa, mu kuma gina garu a Yahuza da Urushalima.
Umarnan da ka umarta ta bakin bayinka annabawa cewa, ‘Ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta, ta ƙazantu da ƙazantar al'umman da take cikinta. Ƙazantarsu ta cika dukan ƙasar.
“Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su, Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne. Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.
Gama kakanninmu, da sarakunanmu, Da shugabanninmu, da firistocinmu, Ba su kiyaye dokarka ba. Ba su kasakunne ga umarnanka da gargaɗinka ba. Da waɗannan ne kake zarginsu.