Ezra 9:1 - Littafi Mai Tsarki1 Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |