Ezra 8:1 - Littafi Mai Tsarki1 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. Wannan kuwa shi ne lissafin asalin waɗanda suka komo tare da ni daga Babila a zamanin sarautar sarki Artashate. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gershom shi ne shugaban iyalin Finehas, Daniyel shi ne na iyalin Itamar, Hattush ɗan Shekaniya, shi ne na iyalin Dawuda. Zakariya shi ne na iyalin Farosh, ya zo da iyalinsa mutum ɗari da hamsin. Eliyehoyenai ɗan Zarahiya, shi ne na iyalin Fahat-mowab, tare da shi kuma akwai mutum ɗari biyu. Shekaniya ɗan Yahaziyel, shi ne na iyalin Zattu, tare da shi akwai mutum ɗari uku. Ebed ɗan Jonatan, shi ne na iyalin Adin, tare da shi akwai mutum hamsin. Yeshaya ɗan Ataliya, shi ne na iyalin Elam, yana tare da mutum saba'in. Zabadiya ɗan Maikel, shi ne na iyalin Shefatiya, yana tare da mutum tamanin. Obadiya ɗan Yehiyel, shi ne na iyalin Yowab, yana tare da mutum ɗari biyu da goma sha takwas. Shelomit ɗan Yosifiya, shi ne na iyalin Bani, yana tare da mutum ɗari da sittin. Zakariya ɗan Bebai, shi ne na iyalin Bebai, yana tare da mutum ashirin da takwas. Yohenan ɗan Hakkatan, shi ne na iyalin Azgad, yana tare da mutum ɗari da goma. Elifelet, da Yehiyel, da Shemaiya, su ne na iyalin Adonikam (su ne suka zo daga baya), suna tare da mutum sittin. Utai da Zabbud, su ne na iyalin Bigwai, suna tare da mutum saba'in.
Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyu Zuriyar Ara, mutum ɗari bakwai da saba'in da biyar Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812) Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyar Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyu Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222) Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056) Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwas Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar.