Ezra 7:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.