Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 7:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Duk wanda bai yi biyayya da shari'ar Allahnka ba, ko shari'ar sarki, sai a yi masa hukunci mai tsanani, ko na mutuwa, ko na kora, ko na ƙwace dukiyarsa, ko na kurkuku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 7:26
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na kuma umarta, cewa duk wanda ya karya wannan doka, sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa'an nan a mai da gidansa juji.


Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, “Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.


Don haka Allah zai ɓata ka har abada, Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka, Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.


Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.


Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al'umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”


“ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”


Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, mu kuwa muna tare da kai. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi shi.”


Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama'ar da suka dawo daga zaman talala. Haka shugabanni da dattawa suka umarta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ