Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 7:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma'aikatan wannan Haikali na Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 7:24
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra'ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma'aikatan Haikali, suka taho Urushalima.


Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.


Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.


Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.


Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.


Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba.


Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ