Ezra 6:8 - Littafi Mai Tsarki8 Ina umartarku ku biya wa dattawan Yahuza kuɗin sāke ginin Haikalin nan na Allah, a biya mutanen nan cikakken kuɗin aiki daga baitulmalin sarki, wanda yake a lardin Yammacin Kogi, ba tare da ɓata lokaci ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |