Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 6:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sarki Dariyus ya ce, “Zuwa ga Tattenai, mai mulkin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu, wato ma'aikatan hukuma na lardin Yammacin Kogi, ku nisance su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Saboda haka Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai, da ku masu muƙami na yankin, ku bar wurin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 6:6
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wannan lokaci kuma, sai Tatenai, mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka je wurinsu suka yi magana da su, suka ce, “Wa ya ba ku izini ku gina Haikalin nan, har ku gama wannan garu?”


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma'aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.


Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.


Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”


Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”


Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”


Sa'an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda, da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma'aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,


“Ku ƙyale aikin Haikalin nan na Allah kawai, ku ƙyale masu mulkin Yahudawa da dattawan Yahudawa, su sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.


Saboda maganar sarki Dariyus, sai Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka aikata abin da sarki Dariyus ya umarta da aniya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ