Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 6:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 6:16
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama'a suka keɓe Haikalin Allah.


Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.


A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki.


Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima,


Na yi murna sa'ad da suka ce mini, “Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”


Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.


Sa'an nan firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron Haikali, da mawaƙa da waɗansu da dama daga cikin jama'a, da ma'aikatan Haikali, da dukan Isra'ilawa suka zauna a garuruwansu.


Sa'ad da abokan gāban Yahuza da Biliyaminu suka ji waɗanda suka komo daga bauta suna gina Haikalin Ubangiji Allah na Isra'ila,


Saboda haka an yi babban farin ciki a Urushalima, gama tun daga zamanin Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ba a yi wani abu kamar haka a Urushalima ba.


Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.


Da haka fa Isra'ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.


Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali.


A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi.


Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.


Sa'an nan ya ce musu, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha ruwan inabi mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi, gama wannan rana tsattsarka ce ta Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin da Ubangiji ya ba ku shi ne ƙarfinku.”


Sa'an nan sarki Sulemanu, tare da Isra'ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.


Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza?


Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.


A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ