Ezra 6:14 - Littafi Mai Tsarki14 Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.