Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 6:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Saboda maganar sarki Dariyus, sai Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka aikata abin da sarki Dariyus ya umarta da aniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Saboda umarnin da sarki Dariyus ya aika, sai Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites da Shetar-Bozenai da abokansu suka yi biyayya da umarnin babu wasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 6:13
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda, da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma'aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,


Mutane da yawa sukan nemi farin jini daga wurin mai mulki, amma Ubangiji ne yake yi wa mutum adalci.


Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, “Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.”


Sarki Dariyus ya ce, “Zuwa ga Tattenai, mai mulkin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu, wato ma'aikatan hukuma na lardin Yammacin Kogi, ku nisance su.


Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma'aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.


Sa'ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.


A wannan lokaci kuma, sai Tatenai, mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka je wurinsu suka yi magana da su, suka ce, “Wa ya ba ku izini ku gina Haikalin nan, har ku gama wannan garu?”


Da iko sarki yake aiki, don haka ba mai iya ce masa, “Don me?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ