Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 6:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincike ɗakin littattafai na Babila, inda aka ajiye takardun shaida.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 6:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al'amari.”


Muna girmama Allah saboda abin da ya rufe, muna girmama sarakuna saboda abin da suka ba da bayaninsa.


domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka gani a littattafan tarihi, cewa wannan birni na tayarwa ne, mai yin ta'adi ga sarakuna da larduna. A nan ne aka ta da hargitsi a dā. Shi ya sa aka lalatar da shi.


A hannun dama na wanda yake zaune a kursiyin kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai.


Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi.


Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.


Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’


Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare ni Suna a Littafin Shari'a.


Ni mahaifi ne ga matalauta, Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.


Na ba da umarni, aka bincika, aka kuwa tarar, cewa wannan birni ya tayar wa sarakuna a dā, an yi tawaye da hargitsi cikinsa.


Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa'an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra'ila magana.”


Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.


“Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra'ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ