Ezra 5:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.