Ezra 5:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 “Saboda haka Sheshbazzar ya so ya aza harsashin gina gidan Allah a Urushalima. Tun daga wancan lokaci har zuwa yau ana kan gina shi amma ba a gama ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.