Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 5:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama'a zuwa Babila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Amma domin kakanninmu sun ɓata wa Allah na sama rai, sai ya bari suka fāɗa cikin hannun Nebukadnezzar mutumin Kaldiya, sarkin Babilon, wanda ya rushe wannan haikali, ya kuma kwashe mutane zuwa Babilon.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 5:12
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.


Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa.


“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?


Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa, Ransa bai ji daɗinsu ba.


A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.


Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai.


Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.


Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su?


A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’


A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.


Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na 'ya'yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,


Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.


Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ