Ezra 4:3 - Littafi Mai Tsarki3 Amma Zarubabel, da Yeshuwa, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila suka ce musu, “Ba abin da za ku yi tare da mu na ginin Haikalin Allahnmu, amma mu kaɗai za mu yi wa Ubangiji Allah na Isra'ila, gini kamar yadda sarki Sairus, wato Sarkin Farisa, ya umarce mu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.