Ezra 4:24 - Littafi Mai Tsarki24 An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 Saboda haka aikin a gidan Allah a Urushalima ya tsaya cik sai a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus sarkin Farisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.