18 “An karanta mini wasiƙar da kuka aiko mana, filla filla.
18 An karanta, an kuma fassara mini wasiƙar da kuma aika.
Suka karanta daga littafin dokokin Allah sosai, suka fassara musu, saboda haka jama'a suka fahimci karatun.
Sarki kuma ya aika musu da amsa ya ce, “Gaisuwa zuwa ga Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, da abokansu waɗanda suke zaune a Samariya da lardin Yammacin Kogi.
Na ba da umarni, aka bincika, aka kuwa tarar, cewa wannan birni ya tayar wa sarakuna a dā, an yi tawaye da hargitsi cikinsa.