Ezra 3:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sai Yeshuwa da 'ya'yansa da danginsa, da Kadmiyel da 'ya'yansa, da 'ya'yan Hodawiya, da 'ya'yan Henadad, duk Lawiyawa ne, suka yi shugabancin aikin ginin Haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.