Ezra 3:11 - Littafi Mai Tsarki11 Da bangirma suka raira waƙa ta yabo da godiya ga ubangiji, suna cewa, “Ubangiji nagari ne, Gama ƙaunarsa marar matuƙa ce, Ta tabbata har abada ga Isra'ila.” Sai mutane duka suka ɗaga murya da ƙarfi suka yabi Ubangiji, saboda an aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Gama shi nagari ne, Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.” Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,