Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra'ila ne.
Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin 'ya'yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu,